LAUYOYI SUN MAKA GWAMNATIN NAJERIYA A KOTU SABODA TILASTAWA MA’AIKATA ALLURAN RIGAKAFIN KORONA
Wasu Lauyoyin da ke karkashin masu fafutukar kare hakkin jama’a da adalci sun shigar da gwamnatin tarayya kara kan dokar da ta Kafa na tilasta wa kowane ma’aikaci nuna shaidar allurar rigakafin cutar Korona kamun a basu izinin shiga ma’aikatun gwamnati.
Tun daga farko gwamnatin tarayya ta ba da sanarwar cewa daga ranar 1 ga watan Disamba, 2021, za a bukaci ma’aikatan su nuna shaidar allurar COVID-19 ko kuma sakamakon gwajin COVID-19 na PCR da aka yi cikin sa’o’ii 72, don samun damar shiga ofisoshinsu, a duk wurare.
A karar da ta shigar gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, gamayyan Lauyoyin sun kalubalanci manufar Suna mai cewa ta sa’ba wa sashe na 37 na kundin tsarin mulkin Najeriya, 1999, da ya bai wa kowane ɗan ƙasa damar keɓanta matsayin lafiyarsa ba tare da tsangoma ko tilasta bayyana shi ba.
www.wtvnigeria.com