LIKITOCI NA CI GABA DA YAJIN AIKI A KASAR ANGOLA
Rahotani da Kasar Angola na cewa sama da kwararrun likitoci 3000 ne suka tsunduma yajin aiki na neman karin albashi da yanayin aiki.
Kungiyar likitocin kasar ta sanar da tsawaita yajin aikin da ta fara a makon jiya, inda
ta baiwa gwamnati wa’adin kwanaki 30 duk da cewa ta fara tattaunawa da hukumomin kasar.
www.wtvnigeria.com