LIKITOCI SUN CE AKALLA MUTANE 15 AKA KASHE A ZANGA-ZANGAR KIN JININ GWAMNATIN SUDAN

LIKITOCI SUN CE AKALLA MUTANE 15 AKA KASHE A ZANGA-ZANGAR KIN JININ GWAMNATIN SUDAN

 

Jami’an tsaro sun harbe akalla mutane 15 tare da raunata wasu da dama yayin da dubban ‘yan ‘Kasar Sudan suka fantsama kan tituna a ranar Laraba a rana mafi muni cikin wata ‘daya da aka shafe ana zanga-zangar adawa da mulkin soja.

 

Masu zanga-zangar sun yi tattaki a babban birnin kasar ta Khartoum da kuma garuruwan Bahri da Omdurman, inda su ka bukaci da a mika Kasar ga hukumomin farar hula tare da gurfanar da shugabannin juyin mulkin ranar 25 ga watan Oktoba

#wtvnigeria

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *