Majalisar Dattawan Najeriya a ranar Laraba ta nemi Shugaba Muhammadu Buhari da ya ayyana ‘yan bindiga tamkar ‘yan ta’adda a fadin Kasar.
Kazalika, majalisar ta nemi shugaban da ya bude cikakken yaki da Yan bindigan, tare da jefa boma-bomai a duk sansanoninsu da anniyar kawar da su a doron Kasa.
Majalisar Dattawan ta kuma nemi Shugaba Buhari da ya bada dokar nemo dukkan sanannun shugabannin ‘yan bindigar ruwa a jallo.
Waɗannan na daga cikin ƙudurin majalisar bayan yin la’akari da ƙudirin da sanata Ibrahim Gobir (Sakkwato ta Gabas) ya gabatar, tare da hadin gwuiwan wasu Sanatoci 8.