MUNA SAMUN NASARA A YAKI DA TA’ADDANCI A JIHAR IMO-Inji CP Hussaini Rabi’u
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Imo, CP Hussaini Rab’u ya baje hajar nasarorin da rundunarsa ta samu a wannan shekarar 2021 mai karewa.
CP Rabi’u yace rundunarsa ta samu nasarar kawar da ‘yan ta’adda, yayinda da yawansu suka shiga hannu.
Haka kuma ya tabbatar da cewa rundunarsa ta gano dimbin miyagun makamai da suka hada da bindigogi da harsasai.
Kwamishinan yace sun samu nasarar kubutar da mutane da dama daga hannun masu garkuwa da mutane tare da kwato abubuwan hawa da suka hada da motoci da babura.
Bugu da kai, ya ce rundunarsa ta shirya tsaf don tabbatar da tsaron rayukka da dukiyoyin al’ummar jihar a bukukuwan Kirsimati da sabuwar shekarar dake tafe.
CP Rabi’u yace don samun nasarar samar da tsaron, rundunarsa ta kulla hadin kai da sarakuna da al’ummomin da aka karfafa ma kafa kungiyoyin sakai.
Haka kuma rundunar ta aika jami’an ta masu aikin asiri a muhimman wurare
don tabbatar da an yi bukukuwan cikin lumana da kwanciyar hankali.
www.wtvnigeria.com