MUTANE 5 SUN RASA RANSU SAKAMAKON ZANGA-ZANGAR ADAWA DA GWAMNATIN KASAR SUDAN
Masu zanga-zangar adawa da gwamnati kasar sudan sun rufe tituna a birnin Khartoum a ranar Juma’a don nuna adawa da barkewar wani tashin hankali da ya yi sanadin mutuwar mutane biyar tare da yin tofin Allah tsine.
A ranar alhamis da ta gabata ne hukumomin kasar suka dau sabbin matakan dakile zanga zangar inda suka katse data na wayar hannu, da duk wata hanyar sadarwa ta wayar tarho, tare da rufe gadojin da suka hade birnin Khartoum da kewayenta, Omdourman da Khartoum-ta arewa.
Rahotani daga Khartoum, babban birnin kasar na cewa jami’an tsaro sun harba barkonon tsohuwa da harsasai masu rai kan dubun dubatar masu zanga-zangar, lamarin da ya jawo mutuwar mutane 5