MUTANE DUBU 500,000 SUN RASA MUHALLINSU A SUDAN TA KUDU SAKAMAKON AMBALIYAR RUWA

MUTANE DUBU 500,000 SUN RASA MUHALLINSU A SUDAN TA KUDU SAKAMAKON AMBALIYAR RUWA
Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutane dubu 500 ne ambaliyar ruwa ta shafa a Sudan ta Kudu.
Kusan rabin kananan hukumomin kasar na cikin ruwa, inda ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haddasa koguna su fashe.
Shugaba Salva Kiir ya ce dukiyarsa da ke kauyensu ta nutse kuma lokaci ya yi da ya kamata ‘yan Sudan ta Kudu su yi aiki tare don magance matsalar jin kai a maimakon fada.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce dubunnan mutane ne ambaliyar ta raba da muhallansu, dabbobinsu da amfanin gona.
Sudan ta Kudu, sabuwar kasa ce da Ke kokarin farfadowa daga mummunan yakin basasa, wanda ya barke ba da dadewa ba bayan samun ‘yancin kai daga Sudan shekaru goma da suka gabata.

GUDUMMAWA:

Tabbatar da tsabtataccen aikin jarida, abu ne da ke da muhimmin amfani wajen wanzuwar zaman lafiya, ilimantar da al’umma kan lamuran yau da kullum, da kuma kauracewa duk wani abinda zai jawo rudani ko tashin hankali. A dalilin haka ne muke bukatar gudummawarku domin dorewar wannan kokarin. Domin bada gudammawa, ga bayanan asusun banki:

Jaiz Bank Account lamba:

0001741269

Wonderland Television ltd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *