MUTUM 3 SUN MUTU YAYINDA WASU DARURUWA SUKA JIKATA SAKA

MUTUM 3 SUN MUTU YAYINDA WASU DARURUWA SUKA JIKATA SAKAMAKON HARBIN KUNAMA

Wasu kunamai a ‘Kasar Masar sun kashe mutane uku a birnin Aswan da ke kudancin kasar, yayinda da wasu ‘karin Mutane 450 suka jIkata, bayan da guguwa mai karfi ta Kwaso su zuwa tituna da gidaje.

Kawo yanzu, ruwan sama mai karfi na yawan kwaso kunama da sauran dabbobi masú rarrafe da suka hada da macizai daga daji zuwa kan tituna.

An samar da karin maganin dafin ga cibiyoyin kiwon lafiya a kauyukan da ke kusa da tsaunuka da hamada, kamar yadda wani jami’in kiwon lafiya ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Al-Ahram.

Jami’in ya kara da cewa an bukaci mutane da su kasance a gidajensu, su guji wuraren da Ke da bishiyoyi da yawa.

Kasar Masar dai gida ce ga manyan bakaken kunamai da suka fi kashe mutane a duniya, saboda dafinsu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *