NAJERIYA TA SHAWARCI MASU SAFARAR KWAYOYI SU TUBA KO SU HADU DA FUSHIN HUKUMA

Shugaban Hukumar Yaki da shan Muggan Kwayoyi ta Najeriya (NDLEA), Birgediya Janar Buba Marwa, mai ritaya, ya shawarci masu safarar muggan kwayoyi da su tuba ko kuma su yi asarar ‘yancinsu da dukiyoyinsu a sabuwar shekara.
Marwa ya ba da wannan shawarar ne a sakonsa na sabuwar shekara, inda ya ce hukumar NDLEA da ma’aikatanta sun shirya tsaf domin kawar da haramtattun kayan maye da masu safarar su daga fadin kasar.