NAJERIYA ZA TA HARAMTA ZIRGA-ZIRGAN JIRAGEN SAMA DAGA KASASHEN BIRTANIYA, KANADA, SAUDI ARABIYA DA AJANTINA
Gwamnatin Najeriya za ta hana zirga-zirgar jiragen sama daga Birtaniya, Kanada, Ajantina da Saudi Arabiya, a matsayin ramuwar gayya ga matakin sanya Najeriya cikin jerin kasashen da suka haramtawa shiga kasashensu Saboda barkewar cutar Omikron Korona.
Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, ne ya bayyana hakan a cikin wani faifan murya da aka fitar, inda ya bayyana cewa kwamitin da Shugaban kasa ya kafa kan COBID-19 zai sanar da dokar hana kasashen uku ranar Litinin ko Talata mai zuwa.
www.wtvnigeria.com