RAHOTANI DAGA SUDAN NA NUNA SOJOJI SUN YI JUYIN MULKI A ‘KASAR

RAHOTANI DAGA SUDAN NA NUNA SOJOJI SUN YI JUYIN MULKI A ‘KASAR

Rahotani daga ‘kasar Sudan na cewa Sojoji sun cafke mafi yawan membobin majalisar ministocin ‘kasar da dimbin shugabannin jam’iyyun da ke goyon bayan gwamnati a ranar Litinin a wani juyin mulkin da sojojin suka yi, in ji wasu majiyoyin siyasa guda uku, lamarin da ya jefa sauyi zuwa dimokradiyya cikin rudani.

An tsare Firayim Minista Abdalla Hamdok kuma an kai shi wani wuri da ba a bayyana ko ina ne ba, bayan ya ki amincewa da fitar da wata sanarwa ta goyon bayan juyin mulkin, in ji ma’aikatar yada labarai.

Sai dai kawo yanzu, babu wani karin bayani daga rundunar sojin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *