Rahoton WTV kan kiwon lafiya ya ankarar da hukumomi a jihar Yobe

RAHOTON WTV KAN RASHIN KULAWA DA MARASA LAFIYA A ASIBITOCIN JIHAR YOBE YA ZABURAR DA MA’AIKATAR KIWON LAFIYA

Biyo bayan rahoto da Gidan Talabijin na WTV ta watsa ranar Talata kan barazana da al’ummar Jihar Yobe Ke fuskanta sakamakon rashin likitoci a manyan asibitocin jihar, Hukumar lafiya ta jihar ta Kafa kwamitin duba yadda ayyuka ke gudana a asibitin kwararru na Birnin Damaturu.

Tuni kwamitin ta Kai ziyarar gani da ido Babban asibitin kwararru na Birnin Damaturu, Cikin daren laraba, kamar yadda WTV ta samu labari.

Haka zalika, mun samu labarin Kwamishinan Lafiya na Jihar Dr Mohammad Ganaya ziyarci Babban asibitin kwararru na Birnin Damaturu, yau Alhamis, inda Babban jami’ar asibitin Dr Aisha Buba ta zaga da shi da tawagarsa. Wakilin WTV a jihar Yobe Anwar Gaidam ne ya hada rahoton.

GUDUMMAWA:

Tabbatar da tsabtataccen aikin jarida, abu ne da ke da muhimmin amfani wajen wanzuwar zaman lafiya, ilimantar da al’umma kan lamuran yau da kullum, da kuma kauracewa duk wani abinda zai jawo rudani ko tashin hankali. A dalilin haka ne muke bukatar gudummawarku domin dorewar wannan kokarin. Domin bada gudammawa, ga bayanan asusun banki:

Jaiz Bank Account lamba:

0001741269

Wonderland Television ltd

Leave a Reply

Your email address will not be published.