RIKICIN ALJERIYA DA FARANSA: ALJERIYA TA HANA JIRAGEN SOJIN FARANSA SHIGA KASAR TA

RIKICIN ALJERIYA DA FARANSA: ALJERIYA TA HANA JIRAGEN SOJIN FARANSA SHIGA KASAR TA

Kasar Aljeriya ta hana jiragen sojan Faransa shawagi a sararin samaniyarta, in ji rundunar sojan Faransa, yayin da takaddamar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu ke kara tsananta.
Matakin na zuwa ne kwana guda bayan da Aljeriya ta kira jakadanta daga birnin Paris, inda ta zargi Faransa da yin katsalandan da ba za a amince da shi ba a harkokin ta.
Aljeriya ta ce tana mayar da martani ne kan kalaman da wata jaridar Faransa ta danganta da Shugaba Emmanuel Macron.
An ambato shi yana cewa tsohon tsarin mulkin Faransa yana karkashin “tsarin siyasar-soja” tare da tarihi mara tushe, kuma Mai ƙiyayya da Faransa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *