RIKICIN KASAR KAMARU YA SA MUTANE SAMA DA DUBU 30,000 TSEREWA ZUWA KASAR CHADI
Sama da mutane 30,000 ne a arewacin Kamaru suka tsere zuwa kasar Chadi sakamakon rikicin da ya barke a karshen mako da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 22, kamar yadda hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.
Wata sanarwa da hukumar ta UNHCR ta fitar a jiya Juma’a daga birnin Geneva ta bayyana cewa, an samu tashin hankali a kauyen Ouloumsa da ke kan iyaka a ranar Lahadin da ta gabata, sakamakon takaddamar da ta barke tsakanin makiyaya, masunta da kuma manoma kan raguwar albarkatun ruwa.
www.wtvnigeria.com