Rundunar Sojin Najeriya ta kori jami’an ta biyu John Gabriel da Lance Cpl Adamu Gideon, wadan da ake zargi da kisan malamin addinin Musulunci a Jihar Yobe, Sheikh Goni Aisami.
Mukaddashin kwamandan Bataliyar 241 RECCE da ke Nguru, ta Jihar Yobe, Lt. Col. Ibrahim Osabo ne ya bayyana hakan yau Asabar bayan karbe kayan aiki daga hannun wadan da ake zargi da kisan.
Kwamandan ya ce za’a mika sojojin da aka kora ga rundunar yan sanda don hukunta su.