SANATA SARAKI YA HALARCI ƊAURIN AUREN ƊIYAR SHEIK BALA LAU

nooow

 

SANATA SARAKI YA HALARCI ƊAURIN AUREN ƊIYAR SHEIK BALA LAU

Tsohon Shugaban majalisar dattawan Nijeriya kuma tsohon gwamnan Jihar Kwara, Dakta Abubakar Bukola Saraki ya halarci ɗaurin auren diyar shugaban kungiyar Izala ta Nijeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau.
Auren wanda aka ɗaura a babban masallacin Juma’a na Sheikh Abubakar Mahmud Gumi dake unguwar Malali a Jihar Kaduna, Jiya, juma’a, ya samu halartar manyan ba’ki da malamai daga sassan Nijeriya.

nooow

Wazirin na Ilorin ya shaidi auren wanda aka kulla tsakanin amarya Rufaida Bala Lau da angonta Tijjani Abdullahi Gabba.
A wani saƙon taya murna da ya ɗora a shafinsa na Facebook, Dakta Saraki ya yi wa ma’auratan fatan alheri tare da addu’ar Allah Ya albarkaci aurensu.

www.wtvnigeria.com

GUDUMMAWA:

Tabbatar da tsabtataccen aikin jarida, abu ne da ke da muhimmin amfani wajen wanzuwar zaman lafiya, ilimantar da al’umma kan lamuran yau da kullum, da kuma kauracewa duk wani abinda zai jawo rudani ko tashin hankali. A dalilin haka ne muke bukatar gudummawarku domin dorewar wannan kokarin. Domin bada gudammawa, ga bayanan asusun banki:

Jaiz Bank Account lamba:

0001741269

Wonderland Television ltd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *