SANATA SARAKI YA JINJINAWA MADUGUN ‘YAN ADAWAR KENYA, RAILA ODINGA, KAN BAYYANA ANIYARSA NA TSAYAWA TAKARAR SHUGABAN KASA
Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Abubakar Bukola Saraki, ya jinjinawa madugun ‘yan adawar Kenya, Raila Odinga, da ya bayyana muradinsa na tsayawa takara a zaben shugaban kasa mai zuwa.
A cikin wani sakon bidiyo na musamman da Odinga ya bukaci Sanata Saraki ya yi wa wakilan jam’iyyar Orange Democratic Movement a lokacin babban taronta, Saraki ya taya Odinga murnar sake bayyana kudurinsa na tsayawa takarar shugancin Kasar tare da yi masa fatan alheri bisa kyakkyawar makoma da ya himmatu wajen samarwa al’ummar Kasar Kenya.
www.wtvnigeria.com