SARKIN BAUCHI YA SAUKE HAKIMAI 4 AKAN RASHIN TSARO

SARKIN BAUCHI YA SAUKE HAKIMAI 4 AKAN RASHIN TSARO

An sauke wasu hakimai hudu da ke karamar hukumar Toro a Jihar Bauchi, bisa zargin sakaci wajen tafiyar da al’amuransu da har ya taimaka wa masu aikata laifuka a yankunansu.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Sulaimanu Adamu, mai dauke da sa hannun sakataren masarautar, Malam Shehu Muhammad.

Sanarwar ta bayyana cewa Hakiman da abin ya shafa sun hada da mai wakiltan Buruku, Turkunyan Biru, Gamawa da na Zomo, duk a karamar hukumar Toro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *