SHUGABA BUHARI YA NEMI TSATTSAURAN HUKUNCI GA LAUYOYI DA KE HANA RUWA GUDU WAJEN TAFIYAR HARKAR SHARA’A

SHUGABA BUHARI YA NEMI TSATTSAURAN HUKUNCI GA LAUYOYI DA KE HANA RUWA GUDU WAJEN TAFIYAR HARKAR SHARA’A

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya yi kira ga bangaren shari’a da su tsara tare da daukar tsauraran matakai kan lauyoyi dake amfani da dabaru wajen jinkirta Shari’a wanda hakan ke kawo cikas ga gudanar da adalci cikin gaggawa a kasar.

Yin hakan Inji Shugaban ya zama tilas wajen kara inganta fannin shari’a da Kuma tabbatar da dimokuradiyyar mai dorewa a kasar, tare da jawo masú neman saka hannun jari daga kasashen waje.

Buhari ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin a Abuja, yayin da yake bude taron alkalan manyan kotunan Najeriya na Shekarar 2021, inda ya samu wakilcin mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo
#wtvnigeria

GUDUMMAWA:

Tabbatar da tsabtataccen aikin jarida, abu ne da ke da muhimmin amfani wajen wanzuwar zaman lafiya, ilimantar da al’umma kan lamuran yau da kullum, da kuma kauracewa duk wani abinda zai jawo rudani ko tashin hankali. A dalilin haka ne muke bukatar gudummawarku domin dorewar wannan kokarin. Domin bada gudammawa, ga bayanan asusun banki:

Jaiz Bank Account lamba:

0001741269

Wonderland Television ltd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *