SHUGABAN AFIRKA TA KUDU YA KAMU DA CUTAR KORONA
Wani gwaji da aka gudanar ranar Lahadi a kan Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya nuna yana dauke da cutar korona, in ji fadar shugaban kasar.
Sanarwar ta ce “Shugaban ya fara jin ba dadi bayan ya bar hidimar tunawa da tsohon mataimakin shugaban kasa FW de Klerk a birnin Cape Town da safiyar lahadi.”
Fadar shugaban ta kara da cewa, “Ramaphosa wanda kawo yanzu ya samu cikakkiyar rigakafin cutar, tuni ya killace kansa a birnin Cape Town, kuma ya mika ragamar mulki ga mataimakinsa David Mabuza na tsawon sati guda”
www.wtvnigeria.com