SHUGABAN MALI YA YI ALKAWARIN FITAR DA JADAWALIN ZABUKA A WATAN JANAIRUN 2022
I
Shugaban gwamnatin Mali da ke karkashin mulkin soja, Kanar Assimi Goita, ya yi wa kungiyar kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS alkawarin samar mata da jadawalin zabe nan da karshen watan Janairun 2022.
Kanar Assimi Goita, wanda ya dau alkawari a wata wasika da ya aika wa Kungiyar ranara lahadi, ya Kuma ba da hujjar dage zaben da kuma gudanar da taron tuntubar kasa wanda ya ce ya zama dole don samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.
www.wtvnigeria.com