SOJIN RUWA SUN KAMA BARAYIN DANYEN MAI 20 A BAYELSA
Rundunar Sojan Ruwa ta Najeriya (NNS) Soroh, ta kama wasu mutane 20 da ake zargin barayin danyen mai ne a cikin wani jirgin ruwa mai lamba MT TIS IV a kogin Akassa, karamar hukumar Brass a Jihar Bayelsa.
Kwamandan NNS Soroh, Commodore Patrick Effah, ne ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a ranar Litinin a Akassa, inda ya ce an kama su ne a ranar 6 ga watan Disamba.
Effah ya ce jirgin na dauke da kusan ganga 4,402 na danyen mai da aka samu ba bisa ka’ida ba wanda kudinsa ya kai Naira Milyan N148, 281, 000.