SOJOJI SUN HALLAKA WASU JAGORORIN YAN BINDIGA A ZAMFARA
An kashe wasu shugabannin ‘yan bindiga da ake nema ruwa a jallo, Alhaji Auta, da Kachalla Ruga a wani daji da ke jihar Zamfara, kamar yadda PRNigeria ta ruwaito.
‘Yan bindigan sun gamu da ajalinsu ne sakamakon harin da wani jirgin saman sojan Nijeriya ya kai dajin Gusami da kauyen Tsamre da ke karamar hukumar Birnin Magaji, a daren juma’a.
Wani jami’in leken asiri na soji ya shaidawa PRNigeria cewa jiragen yakin sun sake kashe yan bindigana da dama, da ke kokarin tserewa, da kuma wadanda suka fake a karkashin bishiyoyi a yankin.