Sojojin Najeriya Sun Kawar da ‘Yan Ta’addan Boko Haram a Kauyen Tunkushe

Sojojin Najeriya sun fatattaki wasu mayakan Boko Haram a wani kwanton bauna da suka yi a kauyen Tunkushe a yankin arewa maso gabashin jihar Borno.
Wata Majiyar Soji ta fada wa kamfanin dillacin labarai na PRNigeria cewa maharan, wanda ana zargin sun fito ne daga kungiyar IS a Yankin Afirka ta Yamma (ISWAP), na sanye ne da kayan sojoji a cikin motoci kirar Hilux guda biyu dauke da manyan bindigogi.
Majiyan ya kara da cewa sojojin bataliya ta 212 ne suka yi musu kwanton-bauna a kauyen Tunkushe, mai tazarar kilomita 20 zuwa Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
“Sojojin Bataliya ta 212 na Nijeriya sun samu nasarar ne a wani mummunan artabu da aka yi wanda ya dauki sama da mintuna 30. Sojoji biyu ne suka ji rauni a yayin arangamar, sa’annan ana iya ganin gawarwakin maharan akalla uku, yayin da sojojin ke ci gaba da bin mambobin kungiyar da suka tsere.
“Kayayyakin da aka kwato daga maharan sun hada da; babbar bindiga guda dake bisa mota, bindiga AK 47, na’uran sadarwa da wasu nau’ikan alburusai. An kuma ga jini da dama a kan hanyar inda sauran maharan suka tsere cikin rudani,” inji majiyan.

GUDUMMAWA:

Tabbatar da tsabtataccen aikin jarida, abu ne da ke da muhimmin amfani wajen wanzuwar zaman lafiya, ilimantar da al’umma kan lamuran yau da kullum, da kuma kauracewa duk wani abinda zai jawo rudani ko tashin hankali. A dalilin haka ne muke bukatar gudummawarku domin dorewar wannan kokarin. Domin bada gudammawa, ga bayanan asusun banki:

Jaiz Bank Account lamba:

0001741269

Wonderland Television ltd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *