SOJOJIN SUDAN SUN MAIDO DA HAMBARARREN FIRAYAM MINISTAN ‘KASAR, KAN MUKAMINSA BAYAN JUYIN MULKI
An maido da hambararren Firaministan Sudan, Abdalla Hamdok, kan mukaminsa bayan juyin mulkin da aka yi a watan da ya gabata, da ya jawo tsare shi.
Jim ‘kadan bayan sako shi ranar Lahadi, an nuno Abdalla Hamdok a gidan talabijin yana sanya hannu kan sabuwar yarjejeniyar raba madafun iko da jagoran juyin mulkin, Janar Abdel Fattah al-burhan.
Sai dai gamayyar kungiyoyin farar hula da ta zabi Mr Hamdok a matsayin firayam Ministan shekaru biyu da suka wuce ta ki amincewa da wata sabuwar yarjejeniya.