TA’ADDANCIN ‘YAN BOKO HARAM A KARAMAR HUKUMAR SHIRORO NA TILASTAWA IYAYE CIRE ‘YA’YANSU A MAKARANTU

TA’ADDANCIN ‘YAN BOKO HARAM A KARAMAR HUKUMAR SHIRORO NA TILASTAWA IYAYE CIRE ‘YA’YANSU A MAKARANTU-Inji Gwamnatin Jihar Neja
Gwamnatin Jihar Neja ta sanar da cewa ‘Yan ta’adda a karamar hukumar Shiroro da ke jihar na tilastawa iyaye janye ‘ya’yansu daga makarantu tare da yin watsi da umarnin gwamnati.
A gefe guda kuma, ‘yan ta’addan sun koma kona amfanin gonakin al’umma saboda sun ki biyan harajin da suka dora musu.
Sakataren gwamnatin jihar, Ahmed Ibrahim Matane ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Minna, babban birnin jihar.
Ya ce wadannan abubuwan na faruwa ne a garuruwan Kwaki, Kusaso, Kawure, Chikuba, Kurebe, Madaka, Farin-Dutse, Falali da Ibbru

May be an image of 1 person, sitting and standing

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *