TAKAITATTUN LABARU

TAKAITATTUN LABARU:

 

~A Najeriya, daruruwan mazauna yankunan kan iyaka da Jihar Taraba sun tsere daga gidajensu bayan kashe mutane 11 ciki har da wani basaraken gargajiya da ‘yan awaren Ambazoniya daga Kudancin Kamaru suka yi.

 

~An tsaurara matakan tsaro a sakatariyar jam’iyyar APC mai mulki a Abuja, bisa zargin zanga-zanga da wasu fusatattun ‘yan jam’iyya suka shirya gudanarwa.

 

~Kungiyar daliban Najeriya (NANS) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da su zauna a teburin tattaunawa domin kaucewa sake shiga yajin aikin.

 

~Akalla Mutane 8 ne suka mutu yayin da wasu 15 suka samu raunuka daban-daban a ranar Larabar da ta gabata a wasu hadurra guda biyu a jihar Ogun.

 

~Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da lalata tiransifoma biyu na lantarki tare da kwashe wasu igiyoyi a unguwar Lapai-Gwari da ke kan titin Kasuwar Kayayyakin gini, a garin Minna.

#wtvnigeriawtvnigeria

GUDUMMAWA:

Tabbatar da tsabtataccen aikin jarida, abu ne da ke da muhimmin amfani wajen wanzuwar zaman lafiya, ilimantar da al’umma kan lamuran yau da kullum, da kuma kauracewa duk wani abinda zai jawo rudani ko tashin hankali. A dalilin haka ne muke bukatar gudummawarku domin dorewar wannan kokarin. Domin bada gudammawa, ga bayanan asusun banki:

Jaiz Bank Account lamba:

0001741269

Wonderland Television ltd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *