TARON DA AKA ‘DORAWA ALHAKIN BADA SHAWARAR JADAWALIN DEMOKRADIYYA A MALI TA CE A JINKIRTA ZABE HAR ZUWA SHEKARU 5
Wani taro a Mali da aka dorawa alhakin ba da shawarar jadawalin gudanar da zabuka bayan juyin mulkin da sojoji suka yi, ta bada shawarar a jinkirta zaben da aka shirya yi a watan Fabrairu zuwa tsakanin watanni shida da shekaru biyar nan gaba, saboda matsalolin tsaro.
Tun farko dai gwamnatin rikon kwaryar kasar Mali ta amince da gudanar da zabe a watan Fabrairun shekarar 2022, watanni 18 bayan da bangaren soji karkashin jagorancin Kanar Assimi Goita ya hambarar da gwamnatin shugaba Boubacar Ibrahim Keita, sai dai daga dukkan alamu hakan ya ci tura.
Kungiyar ECOWAS wadda ita ce babbar kungiyar siyasa da tattalin arziki a yammacin Afirka ta sanya takunkumi kan shugabannin da suka yi juyin mulki, tare da yin alkawarin tsananta takunkumin matukar kasar Mali ba ta samar da wani shiri na zaben watan Fabrairu kafin karshen watan Disamban 2021 ba.