TSOHON ‘DAN TAKARAR SHUGABAN KASAR NAJERIYA, BASHIR TOFA YA RASU

Tsohon dan takarar shugaban kasa na rusasshiyar jam’iyyar NRC a jamhuriya ta uku da aka soke a shekarar 1993, Alhaji Bashir Othman Tofa, ya rasu.
Marigayi Bashir Tofa ya rasu ne da sanyin safiyar yau litinin, sakamakon rashin lafiya, kamar yadda wani na kusa dashi, Magaji Galadima ya tabbatar.
An haifi marigayi Bashir Othman Tofa, dan siyasa kuma dan kasuwa, a watan Yunin shekarar 1947, kuma kawo yanzu ya kasance shugaban kungiyar dattawan jihar Kano.