WANI ‘DAN TA’ADDAN IPOB YA GAMU DA FUSHIN HUKUMA A JIHAR IMO

WANI ‘DAN TA’ADDAN IPOB YA GAMU DA FUSHIN HUKUMA A JIHAR IMO

Rundunar ‘yan sandan jihar Imo ta samu nasarar halaka wani dan ta’addan kungiyar aware ta IPOB da ta dade tana nema ruwa a jallo mai suna uchenna Chukwu.

Wannan na kunshe ne a cikin wata takardar manema labarai mai dauke da sa hannun Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar CSP Michael Abbattam wadda aka aiko ma WTV.

A cewar takardar Uchenna Chukwu ya dade yana hada baki a wajen kisan jami’an ‘yan sanda da kone ofisoshinsu kuma yana cikin jerin manyan’ yan ta’addan kungiyar awaren IPOB da rundunar ke nema a jallo.

Takardar tace sai da aka yi musayar wuta tsakanin ‘yan sanda da ‘yan IPOB kafin a kashe Uchenna inda da yawansu suka tsere da raunukan harbi.

A lokacin da Kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Hussaini Rabi’u ke jinjina ma jami’an tsaro ya gode ma al’ummar jihar kan goyan bayan da suke bayar wa tare da kira gare su da su cigaba da taimaka ma rundunar da muhimman bayanai.

GUDUMMAWA:

Tabbatar da tsabtataccen aikin jarida, abu ne da ke da muhimmin amfani wajen wanzuwar zaman lafiya, ilimantar da al’umma kan lamuran yau da kullum, da kuma kauracewa duk wani abinda zai jawo rudani ko tashin hankali. A dalilin haka ne muke bukatar gudummawarku domin dorewar wannan kokarin. Domin bada gudammawa, ga bayanan asusun banki:

Jaiz Bank Account lamba:

0001741269

Wonderland Television ltd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *