WASU TAGWAYEN BOMA-BOMAI SUN TASHI A SANSANONIN MAJALISAR DINKIN DUNIYA DA KE KASAR MALI

Wasu boma-bomai guda biyu sun tashi a sansanonin Majalisar Dinkin Duniya a garin Gao da ke arewacin Kasar Mali a ranar Lahadin da ta gabata, inda suka yi barna amma ba a samu asarar rai ba.
Lamarin da ya auku da sanyin safiyar ranar lahadi, ya girgiza barikin tawagar Majalisar Dinkin Duniya da ke kasar Mali, mai suna MINUSMA, inda hakan ya tilasta wa mazauna wurin neman mafaka na tsawon sa’o’i biyu.
Mai magana da yawun sansanonin Majalisar Dinkin Duniya ta MINUSMA, Myriam Dessables, ce ta tabbatar da harin.