WASU ‘YAN BINDIGA SUN MAKALE A GIDAN YARIN JOS BAYAN SUN KAI HARI A CIBIYAR
Rahotani daga Jos, Jihar Filato na cewa wasu ‘yan bindiga da suka kai hari Gidan Yarin dake tsakiyar birnin sun makale a ciki sakamakon kewaye Cibiyar da Jami’an tsaro su kayi.
Mai Magana da yawun Hukumar dake kula da gidajen yari na Kasa, Francis Enobore, wanda ya tabbatar da faruwar Lamarin yace ‘yan bindigan dauke da manyan makamai sun kai harin ne da yammacin lahadi inda suka yi musayar wuta da masú gadin cibiyar kamun su ka kusa ciki.
Francis ya Kara da cewa “Ko da yake sun samu shiga gidan yarin, amma yanzu haka Jami’an tsaro sun kewaye cibiyar ta yadda babu hanyar fita, Kuma an shawo kan lamarin. Za mu fito da ƙarin Bayani, Nan Bada jimawa ba”, Inji shi