WASU ‘YAN KAMARU SUN ZARGI SOJIN KASAR DA ‘KONA MUSU GIDAJE
Wasu mazauna garin Bamenda da ke arewa maso yammacin Kamaru sun zargi sojojin kasar da kona musu gidaje da wuraren kasuwanci.
Yankin dai na tsakiyar rikicin ‘yan aware ne da aka shafe shekaru biyar ana gwabzawa wanda ya raba dubban daruruwan matsugunai tare da tilasta rufe yawancin makarantu a yankunan da ake kira Anglophone na kasar.
Mazauna yankin sun ce sojoji sun kona kadarorin a Bamenda a ranar Larabar da ta gabata a matsayin martani ga harin kwantan bauna da ‘yan tawaye suka kai musu.
Kawo yanzu hukumomin Kamaru ba su ce komai ba kan zargin.