Yadda Al’ummar Musulmi Suka Cika Birnin Bajoga, Ta’aziyyar Rasuwar Sarkin Funakaye, Mu’azu Muhammad Kwairanga III
An yi janai’ar Sarkin Funakaye, Mu’azu Muhammad Kwairanga III, yau Lahadi a garin Bajoga, dake karamar hukumar Funakaye ta jihar Gombe.
Sarkin Funakaye Mu’azu Muhammad Kwairanga III ya rasu ne a daren ranar Asabar, a garin Bajoga.
Gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya da mukarraban gwamnati hada da sauran sarakuna a jihar Gombe sun halarci sallar jana’izar da aka gudanar a babban masallacin fadar sarkin Funakaye.
Sanarwar da Darakta Janar na yada labarai na Gwamnatin Gombe Ismaila Uba Misilli ya fitar, ta ce marigayin ya rasu yana da shekaru 45 a duniya.
Gwamna Inuwa Yahaya ya nada maragayin Alhaji Muazu Muhammad Kwairanga a matsayin sarkin Funakaye a watan Mayun 2021, kafin rasuwar sa jiya Asabar 27th August, 2022.
Gwamna Inuwa Yahaya ya mika sakon ta’aziyya da alhinin rasuwar sarkin, tare da addu’ar Allah ya masa rahama.
Tawagar Gwamna Inuwa Yahaya ta hada da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Gombe, Abubakar Mohammed Luggerewo, Sakataren Gwamnatin jihar Gombe, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, Shugaban Ma’aikan Gidan Gwamnati Abubakar Inuwa Kari, kwamishinoni da sauran su.
Birnin Bajoga ta cika saboda yawan al’ummar da suka halarci jana’izar.