YAN BINDIGA NA CIN KARENSU BA BABBAKA A YANKIN SHINKAFI

‘YAN BINDIGA NA CIN KARENSU BA BABBAKA A YANKIN SHINKAFI

 

FB_IMG_1638877532443Rahotanni daga garin Shinkafi na jihar Zamfara na cewa hanyar zuwa Sokoto ta gagari al’umma saboda matsalar ‘yan bindiga dake cin karensu ba babbaka.

Wani mazaunin garin da ya roki a sakaya sunan shi saboda tsaro yace a halin yanzu idan mutum na son zuwa Sokoto daga Shinkafi sai ya zagaya ta Goronyo dake jihar Sokoto don ya tsira da rayuwar shi.

Majiyarmu ta ce a makon da ya gabata, tsakanin Talata da jumu’a ‘yan bindiga sun sace mutane kusan 200, kuma sun kashe wasu da ba a san adadinsu ba, saboda sun hana a dauki gawarwakinsu.

Majiyar ta kara da cewa anga gawarwakin mutane a cikin motoci wadanda ‘yan bindiga suka kashe.

Majiyar ta bayyana cewa amma tsakanin Jumu’a da jiya Lahadi an tura wasu jami’an tsaro kuma al’amurra sun fara sauki.

GUDUMMAWA:

Tabbatar da tsabtataccen aikin jarida, abu ne da ke da muhimmin amfani wajen wanzuwar zaman lafiya, ilimantar da al’umma kan lamuran yau da kullum, da kuma kauracewa duk wani abinda zai jawo rudani ko tashin hankali. A dalilin haka ne muke bukatar gudummawarku domin dorewar wannan kokarin. Domin bada gudammawa, ga bayanan asusun banki:

Jaiz Bank Account lamba:

0001741269

Wonderland Television ltd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *