‘YAN BINDIGA SUN HARBE SARKIN RAFIN GUSAU
Wasu ‘yan bindiga sun harbe wani jigon jamiyyar APC a jihar Zamfara, wanda kuma ya nemi tsayawar takarar gwamna a shekarar 2019, Sagir Hamidu (Sarkin Rafin gusau).
Sagir Hamidu ya hadu da ajakinsa ne akan hanyar Kaduna zuwa Abuja a inda ‘yan bindigar suka harbe shi da marecen yau Lahadi.