YAN BINDIGA SUN KASHE AKALLA MUTANE 25 A KUDU MASO YAMMACIN JAMHURIYYAR NIJAR 

YAN BINDIGA SUN KASHE AKALLA MUTANE 25 A KUDU MASO YAMMACIN JAMHURIYYAR NIJAR

 

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe akalla mutane 25 a kudu maso yammacin jamhuriyar Nijar, a wani samame na baya bayan nan da suka kai kan iyakar kasar da Mali.

 

“Mahara a kan babura sun kai hari a sansanin ‘Yan Sa Kai da ke kusa da kauyen Bakorat a yankin Tahoua a ranar Talata”, in ji Attawane Abeitane, magajin garin Tillia.

 

An dauki tsawon sa’o’i da dama ana musayar wuta kafin jami’an tsaron Nijar su iso inda suka fatattaki maharan, in ji Abeitane.

 

Wani jami’in tsaro ya ce mutum ‘daya kadai ya tsira da ransa Cikin ‘yan Sa kan.

 

“Wadannan ‘yan ta’adda ne da suka fito daga kasashen ketare Kuma suna da yawa. An kashe wasu daga cikinsu, yayinda aka kona baburan su”, in ji Abeitane.

#wtvnigeria

GUDUMMAWA:

Tabbatar da tsabtataccen aikin jarida, abu ne da ke da muhimmin amfani wajen wanzuwar zaman lafiya, ilimantar da al’umma kan lamuran yau da kullum, da kuma kauracewa duk wani abinda zai jawo rudani ko tashin hankali. A dalilin haka ne muke bukatar gudummawarku domin dorewar wannan kokarin. Domin bada gudammawa, ga bayanan asusun banki:

Jaiz Bank Account lamba:

0001741269

Wonderland Television ltd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *