YAN GUDUN 6000 DAGA SENEGAL SUN SHIGA GAMBIA SAKAMAKON WANI RIKICI
Kimanin mutane 6,000 ne suka tsere zuwa Gambiya sakamakon wani rikici da ya barke a cikin makon da ya gabata tsakanin sojoji da ‘yan tawaye a Casamance da ke kudancin Senegal mai makwabtaka da kasar, kamar yadda hukumomin Gambia suka sanar a ranar Asabar.
Rundunar sojin kasar Senegal ta sanar da cewa a ranar 13 ga watan Maris ne ta kaddamar da farmaki kan ‘yan tawaye a Casamance, yankin da Gambiya ta raba da arewacin Senegal.
Sojojin sun yi nuni da cewa “babban manufarsu ita ce tarwatsa sansanonin” jagoran ‘yan tawaye Salif Sadio, dake kan iyakar arewa da Gambia.