‘YAN KWALLO 16 CIKIN 28 NA TAWAGAN KASAR GAMBIYA ZUWA GASAR CIN KOFIN AFIRKA SUN HARBU DA KORONA

Kungiyar kwallon kafa ta Gambia ta soke wasanninta biyu na shirye-shiryen tunkarar gasar cin kofin kasashen Afrika da ke tafe saboda yawan masu dauke da cutar Korona cikin tawagar.
Matakin dai ya zo ne ‘yan sa’o’i kadan kafin su kara da kasar Aljeriya a birnin Doha, na kasar Qatar, yayin da wasar su ta biyu, an shirya ta ne da kasar Syria, ranar Talata, mai zuwa.
“Saboda rashin samun ‘yan wasa 16 daga cikin ‘yan wasa 28, muka soke wasannin sada zumunta da za mu yi gabanin gasar cin kofin Afirka, da Aljeriya da Siriya,” a cewar hukumar kwallon kafar Gambia.