‘YAN SANDA A ABUJA SUN CAFKE WASU ‘BARAYI TARE DA ‘KWATO KWAMFUTOCI 75 DA MOTOCI 7

‘YAN SANDA A ABUJA SUN CAFKE WASU ‘BARAYI TARE DA ‘KWATO KWAMFUTOCI 75 DA MOTOCI 7

Rundunar ‘yan sandan Babban Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja, ta cafke wasu gungun ‘barayi da ke fasa motoci domin sace kayayyaki masu daraja, in da tace ta kwato kwamfutoci 75 da sauran kayayyaki daga hannun wadanda ake zargin.

Da yake bayyana hakan wa manema labaru a Abuja ranar Talata, kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Sunday Babaji, ya ce an kuma kwato motoci bakwai da wasu barayi su ka yi awon gaba da su ta hanyar amfani da makulle da ake ce wa ‘master key’

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *