YAN SANDA SUN HARBA BARKONON TSOHUWA KAN MASU ZANGA-ZANGA A BIRNIN KHARTOUM
‘Yan sandan Kasar Sudan sun harba barkonon tsohuwa kan wasu masu zanga-zanga, da suka yi gangami a kusa da fadar shugaban kasa a birnin Khartoum, babban birnin kasar domin bayyana fushinsu kan yarjejeniyar da sojoji suka kulla da ta mayar da Firaminista Abdalla Hamdok kan mukaminsa.
Dubban mutane ne suka fito kan tituna a birnin Khartoum da sauran garuruwan Sudan, ranar Litininin, a wani bangare na zanga-zangar nuna rashin amincewa da juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Oktoba da kuma yarjejeniyar da ta biyo baya da ta bai wa sojoji damar ci gaba da kasancewa cikin kwamitin rikon kwarya da aka kafa a shekara ta 2019 bayan hambarar da gwamnatin Omar Al- Bashir da ta dade tana mulki.