YAN SANDA SUN TARWASA JERIN GWANON ‘YAN TA’ADDA DA SUKA ‘BATAR DA KAMA A MATSAYIN MASU DAUKAR GAWA

‘YAN SANDA SUN TARWASA JERIN GWANON ‘YAN TA’ADDA DA SUKA ‘BATAR DA KAMA A MATSAYIN MASU DAUKAR GAWA

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Imo CSP Michael Abbatam ya sanar cewa sunyi nasarar tarwatsa wani jerin gwanon ‘yan ta’addan da suka batar da kama a matsayin mutanen dake dauke da gawar wani mamaci.

CSP Abbatam yace al’amarin ya faru ne a ranar 17 ga watan Nuwamba, lokacin da dakarun rundunar suka yi tozali da wata motar safara mai lamba NNE 725 ZG da aka manna hoton wata mata a matsayin gawar da ake dauke da ita kuma motar na tare da rakkiyar babura masu dauke da mutane biyu kowanne.

A lokacin da dakarun ‘yan sandan suke binciken motar sai wani mutum ya bude wuta inda nan take aka mayar da martanin da ya halaka daya daga cikin ‘yan ta’addar kuma aka kama wani dan ta’adda mai suna Odedira Ezuala, inda da yawan
‘yan ta’addar suka tsere da raunukan harbi.

Sanarwar ta ce anyi nasarar gano wata bindigar ‘yan sanda kirar fistol mai lamba 90005 da alburusai a lokacin gumurzun.

Sanarwr ta kara da cewa Kwamishinan ‘yan sandan jihar Imo CP Hussaini Rabiu ya gode ma al’ummar jihar kan goyon bayan da suke bayar wa tare da jinjina ma dakarun rundunarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *