‘YAN TA’ADDA NA KONA GONAR DUK WANDA YA KI BIYAN HARAJI-Inji Manoman Jihar Zamfara

‘YAN TA’ADDA NA KONA GONAR DUK WANDA YA KI BIYAN HARAJI-Inji Manoman Jihar Zamfara
May be an image of 1 person and indoor
Manoman dake yankin Magami ta karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara, sun roki gwamnatin tarayya da ta jihar da su yi ma Allah su kai masu dauki saboda harajin da ‘yan bindiga ke aza masu kafin su bari su debi kayan gonarsu ya wuce hankali.
Wasu manoman da suka nemi a sakaya sunayensu sun ce yanzu takai ‘yan bindigar har gona-gona suke bi idan ba su samu manomi ba su bar sako ga leburori cewa ya bar wani adadin kudi za su dawo su karba in ba haka ba su kone gonar da amfanin dake ciki.
Wani manomi yace sai da ya bada naira dubu 300 kafin su bari ya dauki waken suyar shi.
Manomin ya kara da cewa ‘yan bindigar sun kone gonakin maigidan shi wanda suka nemi ya kara masu wani abu kan naira miliyan daya da dubu 200 da ya ba su, wai don gonakin na shi manya ne kuma suna da yawa.
WTV ta yi kokarin tuntubar rundunar ‘yan sandan jihar don jin gaskiyar al’amarin amma hakan ya faskara.
Masu fashin bakin al’muran yau da kullum suna ganin cewa irin wannan al’amarin karbar haraji na iya jawo ma kasa bala’in karancin abinci da yunwa da kuma karuwar ayukkan ta’addanci, muddin ba a shawo kan lamarin ba.

GUDUMMAWA:

Tabbatar da tsabtataccen aikin jarida, abu ne da ke da muhimmin amfani wajen wanzuwar zaman lafiya, ilimantar da al’umma kan lamuran yau da kullum, da kuma kauracewa duk wani abinda zai jawo rudani ko tashin hankali. A dalilin haka ne muke bukatar gudummawarku domin dorewar wannan kokarin. Domin bada gudammawa, ga bayanan asusun banki:

Jaiz Bank Account lamba:

0001741269

Wonderland Television ltd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *