ZA’A YI KARIN GIRMA NA MUSAMMAN GA JAMI’AN HUKUMAR KASHE GOBARA A LEGAS, FILATO DA KWARA
Hukumar kashe gobara a Najeriya (FFS) ta ce zata karrama wasu jami’an ta da suka taka rawar gani wajen kashe wuta yayin gobara na baya bayan nan da ya auku a jihohin Legas, Kwara da Filato.
Mukaddashin hukumar, Dr Karebo Pere Samson, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da kakakin hukumar, ACF Abraham Paul, ya fitar ranar Alhamis, a Abuja.