ZA’BEN SHUGABANCIN JAM’IYYAR APC A JIHAR ZAMFARA YA BAR BAYA DA KURA
ZA’BEN SHUGABANCIN JAM’IYYAR APC A JIHAR ZAMFARA YA BAR BAYA DA KURA
A jiya asabar ne jam’iyyar APC mai mulki ta kaddamar da za’ben shugabannin Jam’iyyar na reshen Jihar Zamfara.
Sai dai za’ben ya bar baya da ‘kura sakamakon taruka biyu da aka gudanar a Jihar duk a rana d’aya.
Yayinda bangaren Gwamna Bello Matawalle suka zabi Tukur Danfulani a matsayin Sabon Shugaban Jam’iyyar, Sirajo Garba Maikatako ne ya lashe za’ben bangaren Sanata Marafa.
Wakilinmu daga Birnin Gusau ya ruwaito cewa an jima ana takaddamar shugabancin jam’iyya a tsakanin bangaren gwamna Matawalle da na tsohon gwamna Abdulaziz Yari wanda Sanata Kabiru Marafa ke mara ma baya.